Wasu 'Yan Bindiga Sun Bindige Mutane 13 A Kudancin Kasar Senegal
(last modified Sun, 07 Jan 2018 11:12:00 GMT )
Jan 07, 2018 11:12 UTC
  • Wasu 'Yan Bindiga Sun Bindige Mutane 13 A  Kudancin Kasar Senegal

Wasu 'yan bindiga dadi sun bindige alal akalla mutane 13 a wani hari da suka kai garin Ziguinchor da ke kudancin kasar Senegal

Rahotanni daga kasar Senegal din sun jiyo jami'an tsaron suna fadin cewa kisan gillan ya faru ne a garin Ziguinchor da ke yankin  Casamance na kasar Senegal din a can yammacin jiya Asabar.

Jami'an tsaron sun bayyana cewar mutanen da aka kashe din suna yankin ne don tattaro itace girki yayin da 'yan bindiga dadin da aka ce sun kai mutane 15 dauke da makami suka far musu inda suka kashe mutane 13 daga cikinsu da kuma raunana wasu na daban.

Kakakin sojojin kasar Senegal din Kanar Abdoul Ndiaye ya tabbatar da batun kisan da kuma adadin yana mai cewa tuni aka tura sojoji yankin don tabbatar da tsaro a yankin da ke fama da fitina da kuma neman wadanda suka kai wannan hari na ta'addanci.