Sabuwar Gwamnatin Kasar Mali Ta Yi Alkawarin Yakar Rashin Tsaro A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27121-sabuwar_gwamnatin_kasar_mali_ta_yi_alkawarin_yakar_rashin_tsaro_a_kasar
Shugaban kasar Mali ya bayyana cewa yaki da rashin tsaro da masu tsatsauran ra'ayin addini shi ne babban aikin dake gaban sabuwar gwamnatin da aka kafa a kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:15+00:00 )
Jan 08, 2018 15:42 UTC
  • Sabuwar Gwamnatin Kasar Mali Ta Yi Alkawarin Yakar Rashin Tsaro A Kasar

Shugaban kasar Mali ya bayyana cewa yaki da rashin tsaro da masu tsatsauran ra'ayin addini shi ne babban aikin dake gaban sabuwar gwamnatin da aka kafa a kasar.

A yayin zaman farko da ya yi tare da sabuwar gwamnatin kasar karkashin Firaminista Soumeylou Boubèye Maiga, Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta ya tabbatar da cewa babban kalu balen dake jiran sabuwar gwamnatin, tabbatar da tsaro, yaki da masu tsatsauran ra'ayin addini da kuma 'yan ta'adda, karfafa cibiyoyin samar da ruwan sha, da kuma wutar lantarki, tare kuma da daukaka tsarin koyarwa a makarantu boko na kasar.

Shugaba Keita ya bukaci sabon Firaministan kasar tare da ministocinsa da su yi duk wani kokari domin magance matsalar da kasar ke fuskanta, sannan kuma su yi kokarin  kamala  duk wani aiki na ci gaban kasar da tsohuwar gwamnati ta fara ba ta kamala ba.

A ranar 29 ga watan Dicembar shekarar da ta gabata ce Firaministan kasar Mali Abdoulaye Idrissa Maiga ya meka takardar murabus din sa ga Shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keïta, bayan haka sai shugaban kasar ya maye gurbinsa da ministan tsaron kasar Soumeylou Boubèye Maiga. 

Sai dai wasu rahotanni daga kasar ta Mali na cewa bayan murabus din nasa zai jagoranci yakin neman zaben shugaba Ibrahim Boubacar Keita a zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.