Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati A Tunusiya
Al'ummar birnin Tunus na ci gaba da zanga-zangar neman gwamnati ta janye kudirin da ta dauka a game da tsarin tattalin arzikin kasar.
Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya nakalto jami'an 'yan sandan Tunusiya a wannan Talata na cewa; mazauna yankuna biyu na birnin Tunus sun gudanar da zanga-zanga a jiya Talala, tare da neman gwamnati ta janye dokar karin farashi na kayan masrufi a sabuwar shekara ta 2018.
Rahoton ya ce bayan al'ummar birnin Tunus, sama da garuruwa 12 na kasar ne aka gudanar da zanga-zangar, inda saida 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sanya hawaye kafin tarwatsa mahalarta zanga-zangar.
A ranar Litinin da ta gabata, zanga-zangar ta yi sandiyar mutuwar mutum guda a kasar, 'yan adawa a kasar ta Tunsiya sun sha alwashin cewa za su ci gaba da zanga-zanga har sai gwamnati ta janye kudirin da ta dauka na karin haraji da hakan yayi sandiyar hauhawar farashi na kayan masrufi a kasar.
Tun a farkon wannan wata ne Al'ummar kasar Tunusiyan suka fara ganin illar sabbin dokoki na tattalin arzikin kasar da gwamnati ta bullo da su a kasafin kudin shekarar 2018.