Sheikh El-Zakzaky Ya Gana Da Manema Labarai A Karon Farko
(last modified Sat, 13 Jan 2018 15:57:54 GMT )
Jan 13, 2018 15:57 UTC
  • Sheikh El-Zakzaky Ya Gana Da Manema Labarai A Karon Farko

Rahotanni daga Nijeriya sun bayyana cewar shugaban kungiyar Harkar Musulunci a kasar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya gana da manema labarai karon farko tun bayan da aka kama shi shekaru biyu da suka gabata inda ya bayyana cewar yana nan a raye kuma lafiyar lau inji kafafen watsa labaran.

Gidan talabijin din Channels na Nijeriyan, a shafinsa na internet ne ya ba da labarin inda ya ce Sheikh El-Zakzaky ya bayyana wa 'yan jaridar da suka gana da shi cewa yana nan a raye kuma lafiyarsa lau, kamar yadda kuma ya gode wa 'yan Nijeriya din saboda addu'oin da suka yi masa na samun lafiya.

Tashar Channels din ta kara da cewa Sheikh Zakzaky ya bayyana cewar a ranar Litinin din da ta gabata jikin na sa yayi tsanani amma ya ce a halin yanzu da sauki sosai bayan da jami'an  tsaron a karon farko suka bari likitocinsa suka duba shi.

Wannan labarin dai yana zuwa ne a daidai lokacin da wasu kafafen watsa labarai da kuma wasu majiyoyi suke ta yada jita-jitan cewa Sheikh El-Zakzaky din ya rasu sakamakon rashin lafiyar da yake damunsa lamarin da hukumar tsaron farin kaya ta kasar da suke tsare da malamin suka musanta tun a jiya.

Wannan dai shi ne karon farko da mahukuntan Nijeriya din suka bari wasu manema labarai suka gana da Sheik Zakzaky tun bayan da sojoji suka kai hari gidansa da kuma kama shi a karshen shekara ta 2015.

Cikin 'yan kwanakin nan dai mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky din suna ci gaba da gudanar da jerin gwano da zanga-zangogi a wasu garuruwa na Nijeriya din musamman babban birnin kasar Abuja don neman gwamnatin Nijeriya din ta sake Shehin malamin don tafiya neman magani sakamakon labarin da ke cewa jikinsa yayi tsanani sosai.