Rikici Ya Sake Barkewa A Tunusiya Bayan Kwanaki Biyu Na Zaman Lafiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27293-rikici_ya_sake_barkewa_a_tunusiya_bayan_kwanaki_biyu_na_zaman_lafiya
Mummunar zanga-zanga ta sake barkewa a wasu yankuna na birnin Tunis, babban birnin kasar Tunusiya da wasu garuruwa na kasar bayan lafawar zanga-zangar ta kwanaki biyu da al'ummar kasar suke yi don nuna adawarsu da matakan tattalin arziki da gwamnatin kasar ta dauka.
(last modified 2018-08-22T11:31:17+00:00 )
Jan 15, 2018 05:54 UTC
  • Rikici Ya Sake Barkewa A Tunusiya Bayan Kwanaki Biyu Na Zaman Lafiya

Mummunar zanga-zanga ta sake barkewa a wasu yankuna na birnin Tunis, babban birnin kasar Tunusiya da wasu garuruwa na kasar bayan lafawar zanga-zangar ta kwanaki biyu da al'ummar kasar suke yi don nuna adawarsu da matakan tattalin arziki da gwamnatin kasar ta dauka.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar wasu munanan zanga-zangogi sun barke a yankunan Ettadamen da Kram na birnin Tunis din a jiya Lahadi inda matasa suka fito kan tituna don nuna rashin amincewarsu da matakin gwamnati na kara yawan kudaden haraji da farashin kayayyakin masarufi wadanda ta ce ta dauka ne domin cike gibin kasafin kudin kasar.

Rahotannin sun ce jami'an tsaron kasar sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa matasa masu zanga-zanga da suke amfani da duwatsu wajen jifan 'yan sanda da kuma kokarin sanya wuta da kona tayu a ci gaba da zanga-zangogin kyamar gwamnatin da suke yi.

Tun da safiyar jiya Lahadin ne daruruwan mutane suka fito zanga-zangogin nuna adawa da gwamnatin a daidai lokacin da ake bikin zagayowar shekaru bakwai da kifar da tsohuwar gwamnatin kama karya ta hambararren shugaban Zine El Abidine Ben Ali. Ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce an kama kimanin mutane 800 bisa zargin tada tarzoma da lalata kayan gwamnati.