An Ceto Bakin Haure Sama Da Dubu A Teku
Jami'an tsaron gabar ruwan kasashen Italiya da Spain sun sanar da ceto 'yan gudun hijira 1.400 daga kasashen Arewacin Afirka a tekun Baharum a jiya Talata.
Wasu jiragen ruwa na hadin gwiwar jami'an tsaron gabar ruwan kasar ta Italiya da rundunar yaki da fataucin bakin haure ta Kungiyar Tarayyar Turai ta Sophia da kuma Kungiyar Proactiva mai zaman kanta ta kasar Spain sun yi sawu 11 a cikin tekun wajen ceto bakin hauren da suka fito daga kasashen arewacin Afirka.
Bakin hauren sun hada da mata 175 da kananan yara 75 wadanda ke makare a cikin jiragen kwale-kwale marasa inganci guda bakwai inda masu ayyukan ceto suka tarar da gawar wani dan karamin yaro da ya mutu a cikin tafiyar tasu.
A jiya Talata, jami'an tsaron ruwan Libiya sun sanar da ceto wasu bakin haure dake son zuwa kasashen Turai kimanin 475 a gabar ruwan kasar.