Kotu A Nijeriya Ta Tabbatar Da Kungiyar IPOB A Matsayin Kungiyar Ta'addanci
Babbar kotun Tarayya a Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriya ta yi watsi da karar da kungiyar nan ta tsageran Inyamurai masu son kafa kasar Biafra ta IPOB ta shigar inda ta tabbatar da ita a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.
Yayin da yake yanke hukumci kan karar alkalin Kotun Mai shari'a Abdu Kafarari ya ce antoni janar na Nijeriya din yana da hakki kuma ya fi hanyoyin da suka kamata wajen bukatar da a haramta kungiyar don haka yayi watsi da kukan da kungiyar shigar, don haka ya tabbatar da hukumcin da aka yanke a baya a watan Satumban 2017 na sanya kungiyar a matsayin kungiyar ta'addanci.
Haka nan kuma alkalin yayi watsi da ikirarin babban lauyan kungiyar ta IPOB Ifeanyi Ejiofor na cewa an take wa 'yan kungiyar hakkinsu don haka ya bukaci kungiyar ta biya Naira 500,000.
Rundunar sojin Nijeriya ne dai ta ayyana kungiyar ta IPOB a matsayin kungiyar ta'addanci bayan wani fito na fito da suka yi da 'yan kungiyar inda daga baya kotun ta yanke hukuncin cewa kungiyar ta IPOB kungiya ce ta ta'addanci. Hukumcin farko na kotun dai ya zo 'yan kwanaki bayan da shugaban kungiyar Nnamdi Kanu yayi layar zana bayan belinsa da aka bayar da kuma sake shi daga gidan yari saboda zargin cin amanar kasa da ake yi masa tare da wasu abokansa. Har ya zuwa yanzu dai ba a tabbatar da inda ya ke ba.