Tunisiya: Sabuwar Zanga-zangar Tsadar Rayuwa Ta Sake Barkewa
Jan 22, 2018 06:19 UTC
A jiya lahadi a garin al-mutawalli mutane sun rufe tituna tare da kona tayoyi, suna masu kira da a samar musu da aikin yi.
Zanga-zangar ta jiya ta zo ne bayan da aka sami lafawar bore da aka yi a cikin garuruwa masu dama na kasar saboda nuna kin amincewa da tsadar rayuwa.
A farkon watan nan na Janairu ne dai gwamnatin kasar ta Tunisiya ta sanar da karin farashin wasu daga cikin kayan masarufi, da kuma soke tallafin da take bai wa talakawan kasar.
Kusan mutane 1000 ne jami'an tsaron kasar su ka sanar da kamewa.
Tags