Masar Ta Nuna Damuwarta Kan halin Da Arewacin Siriya Ke Ciki.
Ministan harakokin wajen Masar ya bayyana ayyukan sojan Turkiya a garin Afrin na kasar Siriya a matsayin barazana a kokarin da ake yi na magance rikicin kasar.
A yayin tattaunawarsa da Sakataren harakokin wajen Amurka Rex W. Tillerson ta wayar tarho, ministan harakokin wajen Masar Sameh Shoukry ya tabbatar da mahimancin girmama 'yancin kasar Siriya a matsayin dunkulalliyar kasa daga dukkanin bangarorin, tare kuma da kiyaye ci gaba da zubar da jini a kasar.
Shoukry har ila yau ya bukaci goyon bayan hadin kan al'ummar kasar da kuma mutunta kungiyoyin kasar ta Siriya.
A ranar juma'ar da ta gabata ce Dakarun tsaron Turkiya dake kan iyakar kasar da Siriya suka lugudan wuta kan dakarun kungiyar dimukradiyar Kurdawan kasar Siriya a yankin Afrin na jahar Halab dake arewacin kasar.
An bayyana cewa shirin Amurka na aikewa da makamai ga wasu kungiyoyin Kurdawa da kuma basu horon soja domin kafa wata runduna mai kushe da sojoji dubu 30 a arewacin kasar ta Siriya, shi ne ya sanya magabatan birnin Ankara din daukar wannan mataki na Soja.