Martanin Majalisar Dinkin Duniya Kan Shirin Zaben Shugabancin Kasa A Masar
(last modified Thu, 25 Jan 2018 06:31:14 GMT )
Jan 25, 2018 06:31 UTC
  • Martanin Majalisar Dinkin Duniya Kan Shirin Zaben Shugabancin Kasa A Masar

Majalisar Dinkin Duniya ta maida martani kan tsoma bakin rundunar sojin Masar a harkokin siyasar kasar tare da jaddada bukatar gudanar da zabuka a kasar cikin 'yanci.

Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana rashin jin dadin Majalisar Dinkin Duniya kan matakin da rundunar sojin Masar ta dauka na kame Janar Sami Anan mai ritaya dan takarar shugabancin kasar tare da kira kan hanzarta sakinsa domin gudanar da zabuka cikin 'yanci da walwala a kasar.

A sanarwar da rundunar sojin Masar ta fitar a ranar Talata da ta gabata yana dauke da cewa: Kame tsohon Janar na rundunar sojin kasar Sami Anan ya zo ne bayan shelanta kansa a matsayin dan takarar shugabancin kasar kafin samun izinin tsayawa takara a zaben watan Maris na wannan shekara. Kamar yadda rundunar sojin Masar take zarginsa da tunzura al'umma kanta.

Har ila yau gwamnatin Masar ta bayyana cewa: Matakin da Janar Sami Anan mai ritaya ya dauka na shelanta kansa a matsayin dan takarar shugabancin kasar ta Masar yana matsayin tunzura rundunar sojin kasar ce da nufin haifar da sabani tsakaninta da ma al'ummar Masar.

A fili yake cewa: Bukatar Janar Sami Anan mai ritaya ta neman tsayawa takarar shugabancin Masar tana matsayin babbar barazana ce ga Abdul-Fatah Al-Sisi da ya shelanta aniyarsa ta neman sake tsayawa takarar shugabancin Masar a karo na biyu bayan karewar wa'adin mulkinsa na farko. sakamakon haka matakin da rundunar sojin Masar ta dauka kan Janar Sami Anan lamari ne da zai kawar da wannan barazana ga Abdul-Fatah Al-Sisi. Haka nan wasu rahotonni suna bayyana cewa: Matsin lamba ne ya tilastawa sauran 'yan takarar shugabancin kasar ta Masar janyewa daga kan aniyarsu ta tsayawa takarar ciki har da Ahmad Shafiq tsohon fira ministan kasar.

Ana sa-ran gudanar da zaben shugaban kasa a Masar a watan Maris na wannan shekara ta 2018, inda a ranakun 16 zuwa 18 al'ummar Masar mazauna kasashen waje zasu fara kada kuri'unsu, sannan a ranakun 26 zuwa 28 a gudanar da zabukan a duk fadin kasar ta Masar.