An Yanke Intarnet Gabanin Zanga-zanga A Chadi
Jan 25, 2018 10:39 UTC
Rahotanni daga Chadi na cewa an yanke hanyoyin sadarwa na intarnet a cikin daren jiya gabanin wata zanga zanga da kungiyoyin fara suka kira a kasar.
A yau Alhamis ne kungiyoyin fara hula a kasar suka shirya gudanar da zanga zanga nuna bacin rai dangane da hauhawar farashin man fetur da tsadar rayuwa da katse wasu kudaden alawus alawus.
An kira zanga zangar dai a kusan ilahirin lardunan kasar.
Bayanai daga kasar na cewa an karfafa kwararen matakai na tsaro da jibge tarin jami'an tsaro a manyan tutunan N'Djamena babban birnin kasar.
An kuma rufe makarantun boko saboda halin da ake ciki.
Wannan dai na zuwa ne bayan wani yajin aiki da 'yan sufiri suka gudanar.
Tags