Mali : An kai wani sabon hari a barikin Sojojin kungiyar turai
Wasu 'yan bindiga sun kai hari a sansanin koyar da aikin soja na kasashen turai dake birnin Bamako na kasar Mali
Jaridar Le figaro ta kasar Faransa ta nakalto wani jami'in ma'aikatar tsaron Mali na cewa 'yan bindiga sun kai hari a sansanin koyar da aikin soja na sojojojn kasashen Turai dake birnin Bamako a jiya Litinin, saidai sun kamu da martani mai tsanani daga bangaren dakarun tsaron Mali gami da na kasashen turai da hakan ya tilasta musu ja da baya, bayan da aka hallaka daya daga cikinsu.
Irin wadannan hare-hare da ake kaiwa a kasar ta Mali musaman ma a birnin Bamako da kuma arewacin kasar shi ke nuna cewa har yanzu kasar ta Mali na fama da matsalar tsaro.
Tun a shekarar 2012 ne kasar ta Mali ta fuskanci juyin milki,bayan haka, kungiyoyin 'yan tawaye da na 'yan ta'adda suka mamaya wani bangare na arewacin kasar, saidai bayan shigar Dakarun tsaron kasashen Afirka da na Faransa sun samu nasarar kwato yankin daga hanununsu, bayan shirya zabe da kuma kafa sabuwar Gwamnati,an cimma yarjejjeniyar sulhu tare da wasu kungiyoyin 'yan tawayen arewacin kasar domin samar da sulhu da kuma konciyar hankali a kasar.