Mali : Fashewar Nakiya Ta Yi Ajalin Mutum 26
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27645-mali_fashewar_nakiya_ta_yi_ajalin_mutum_26
Hukumomi a kasar Mali sun ce kawo yanzu mutane 26 ne suka rasa rayukansu bayan da wata motar sufirin fasinja ta taka wata nakiya a tsakiyar kasar.
(last modified 2018-08-22T07:01:20+00:00 )
Jan 26, 2018 01:36 UTC
  • Mali : Fashewar Nakiya Ta Yi Ajalin Mutum 26

Hukumomi a kasar Mali sun ce kawo yanzu mutane 26 ne suka rasa rayukansu bayan da wata motar sufirin fasinja ta taka wata nakiya a tsakiyar kasar.

Alkaluman wadanda na wucin gadi ne sun ce mutanen da lamarin ya rusa dasu wadanda galibi fararen hula ne sun hada da 'yan kasar ta Mali da kuma na Burkina faso.

Motar dai ta fito ne daga Burkina Faso kuma za ta a wajen wani baje koli a yankin Boni dake jihar Mopti a kasar Mali.

Har kawo yanzu dai ba'a samu wani da ake zargi da aikata hakan, ko kuma wanda ya dauki alhakin hakan.

Dama kafin hakan da sanyin safiyar jiya Alhamis wasu mutane sun farmawa sojojin kasar ta Mali a kusa da lardin Yuwaru dake yankin, inda suka kashe  sojojin 2, koda yake rundinar sojin kasar ta ce ta hallaka bakwai daga cikin maharan wadanda ta danganta da 'yan ta'adda.