An Kashe Mutane 16 A Arewacin Kasar Mali
Jami'an tsaron kasar Mali sun sanar da cewa kimanin mutane 16 ne suka rasa rayukansu a yayin wani hari da wani gungun masu dauke da makamai suka kai arewacin kasar.
Kafar watsa labaran Assabah ya nakalto jami'an tsaron Mali na cewa a safiyar wannan Asabar wasu gungun 'yan bindiga sun kai hari kan wani sansanin soja dake kusa da garin Tumbuktu dake arewacin,inda nan take suka kashe sojoji 14.
Binciken farko sun tabbatar da mutuwar maharan biyu tare sojojin 14,tare da jikkata wasu 17 na daban.
A cikin 'yan shekarun nan, kasar ta Mali ta fuskanci hare-haren kungiyoyi masu dauke da makamai a arewacin kasar.
Tun bayan da Sojoji suka kifar da Gwamnati shekarar 2012 a kasar ta Mali, wasu kungoyoyi suka dauki makamai a arewacin kasar, a farkon shekarar 2013 ne Sojojin kasar Faransa da MDD suka shiga kasar ta Mali domin taimakawa sojojin kasar na fatattakar 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayin addini da suka mamaye wasu yankunan arewacin kasar.