Kasashen Afrika Sun Kuduri Anniyar Dawo Da Zaman Lafiya A Nahiyar
Jan 28, 2018 12:09 UTC
Shuwagabannin Afrika wadanda a halin yanzu suke gudanar da taronsu na 30 a birnin Adisababa na kasar Ethiopia sun kuduri anniyar tabbatar da zaman lafiyar a nahiyar, da kuma shiga a dama da su wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.
Kamfanin dillancin labaran Anatolia ya bayyana cewa shuwagabannin sun kuduri wannan anninyar ce a taron na Adis Ababa, sun kuma kara da cewa zasu yi kokarin kauda duk abin da zai hana fahintar juna a tsakanin kasashen yankin don ganin sun cimma wannan manufar.
Rahoton ya kara da cewa muhimman lamurra da kasashen zasu sa a gaba don cimma wannan manufar sun hada da Safarar mutane, fasa kwaurin kwayoyi da kuma yaki da ayyukan ta'addanci.
Tags