Palasdinu: Wani Matashin Bapalasdine Ya Yi Shahada A Yammacin Kogin Jordan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27779-palasdinu_wani_matashin_bapalasdine_ya_yi_shahada_a_yammacin_kogin_jordan
Ma'aikatar lafiya ta Palasdinu ce ta sanar da shahadar Haitham Abu Na'im dan shekaur 16 bayan da 'yan sahayoniya suka harbe shi.
(last modified 2018-08-22T11:31:21+00:00 )
Jan 30, 2018 19:00 UTC
  • Palasdinu: Wani Matashin Bapalasdine Ya Yi Shahada A Yammacin Kogin Jordan

Ma'aikatar lafiya ta Palasdinu ce ta sanar da shahadar Haitham Abu Na'im dan shekaur 16 bayan da 'yan sahayoniya suka harbe shi.

Tun a karshen 2017 ne al'ummar palasdinu suka fara  bore Intifadha na kare birnin Kudus, wanda shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a matsayin babban birnin haramtacciyar Isra'ila.

Kawo ya zuwa yanzu adadin Palasdinawan da suka yi shahada sun kai 20 yayin da wasu fiye da 1000 suka jikkata.

Bugu da kari da akwai wasu daruruwan Palasdinawan da ake tsare da su a gidajen kurkuku.