Nijar: Boko Haram Sun Kai Hari A Garin Chétimari
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato majiyar tsaron Nijar na cewa a yau talata ne mayakan kungiyar da suke kan babura 10 suka kai harin akan sansanin soja da ke garin Chétimari
Majiyar ta ce maharan na Bokoharam sun janye bayan da suka fuskanci tirjiya mai tsanani daga sojojin da ke sansanin.
Garin Chétimari yana da nisan kilo mita 20 ne daga Diffa a kudu maso gabacin kasar ta Nijar.
A tsakiyar watan nan na Janairu ma dai, maharan na Bokoharam sun kai hari a yankin Toummour da ke gabacin Diffa a gabar tafkin Chadi tare da kashe sojojin kasar 7 da jikkata wasu 17.
Yankin Diffa yana daga cikin yankunan da kungiyar ta Bokoharam take yawan kai wa hare-hare a cikin Jamhuriyar Nijar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga 2015 zuwa 2017 Kungiyar Bokoharam ta kashe fararen hula 582 a cikin hare-hare 244 da ta kai a yankin Diffa.