Ziyarar Shugaban Kasar Faransa A Tunusiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27817-ziyarar_shugaban_kasar_faransa_a_tunusiya
Shugaban kasar Faransa ya fara ziyarar aiki a Tunusiya a daidai lokacin da kasar ke fuskantar zanga-zangar adawa da gwamnati sanadiyar matsin tattalin arziki.
(last modified 2018-08-22T11:31:22+00:00 )
Jan 31, 2018 18:17 UTC
  • Ziyarar Shugaban Kasar Faransa A Tunusiya

Shugaban kasar Faransa ya fara ziyarar aiki a Tunusiya a daidai lokacin da kasar ke fuskantar zanga-zangar adawa da gwamnati sanadiyar matsin tattalin arziki.

Tashar Talabijin din France 24 ta habarta cewa a wannan Laraba ce Shugaban kasar Faransa Emanuel Macron zai fara ziyarar aiki a kasar Tunusiya, bayan da a kwashe makonni biyu ana zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar.

Kuma a wannan Laraba ce ake sa ran Shugaba Macron na Faransa zai gana da shugaba Beji Caid Essebsi na Tunusiya tare da Piraministan kasar Youssef Chahed.

Wannan ziyara ta shugaban kasar Faransa na zuwa ne a daidai lokaci da gwamnatin tunusiya ke fuskantar matsin lamba daga al'ummar kasar saboda matsin tattalin arziki da kuma rashin aiki yi da 'yan kasar ke fuskanta, to saidai ita Faransa na kokarin ci gaba da mamayen harakokin siyasa, tattalin arziki da al'adu kasar ta Tunusiya.

Kasashen Larabawa na yammacin Afirka da suka hada da maroco, Aljeriya, Tunusiya da Murtaniya na a matsayin mashigar kasar Faransa ga kasashn Afirka domin haka ne ma shughaban  kasar ta Faransa yake kai ziyara kasashen Maroco, Aljeriya da Tunusiya watani bayan hawansa kan karagar milki.