Libiya : An Hana 'Yan Yankin Da Ya Goyi Bayan Ghaddafi Komawa Gida
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i27837-libiya_an_hana_'yan_yankin_da_ya_goyi_bayan_ghaddafi_komawa_gida
A Libiya dubban iyalai ne na birnin Tawarga da suka bar yankin bayan hambarar da mulkin tsohon shugaban kasar, Mua'mmar Ghaddafi, aka hana su komawa gida, kamar yadda wata yarjejeniya da suka cimma da gwamnatin hadin kan kasar ta tanada.
(last modified 2018-08-22T11:31:22+00:00 )
Feb 01, 2018 16:50 UTC
  • Libiya : An Hana 'Yan Yankin Da Ya Goyi Bayan Ghaddafi Komawa Gida

A Libiya dubban iyalai ne na birnin Tawarga da suka bar yankin bayan hambarar da mulkin tsohon shugaban kasar, Mua'mmar Ghaddafi, aka hana su komawa gida, kamar yadda wata yarjejeniya da suka cimma da gwamnatin hadin kan kasar ta tanada.

A watan Disamba da ya gabata ne gwamnatin hadaka ta kasar ta sanar da cimma yarjejeniya da mutanen na birnin Tawarga wandanda suka goyi bayan hambararen shugaban kasar, da kuma mayakan dake rike da iko da birnin Misrata, kan su koma yankinsu a watan Fabariru nan.

Saidai a lokacin da suka isa yankin a yau sun ci karo da gugun mayaka da suka hana su shiga brinin.

A cewar tashar talabijin ta ''Libya Channel'' sama da iyalai 600 ne jami'an tsaron birnin Bani Walid suka tsare a kudu maso gabashin Tripoli saboda dalilai na tsaro.

Majalisar shawara ta Misrata dai ta bukaci gwamnatin hadaka ta kasar data gaggauta daukar mataki na dage lokacin komawar mutanen yankinsu, saboda hakan ya sabawa yarjejeniyar da aka cimma.