An Sake Kashe Sojojin Kamaru A Arewa Maso Yamma
An kashe wasu jami'an tsaro Jandarma biyu na Jamhuriya Kamaru a yankin masu magana da turancin ingilishi a arewa maso yammacin kasar.
Bayanai daga kasar na cewa 'yan fafatukar a ware masu dauke da makamai sun akai hari a wani shingen soji na yankin Bingo inda suka raunana jami'an jandarma biyu.
Wata majiyar soji ta shaidawa kamfanin dilancn labaren AFP cewa, sojojin biyu sun cika a asibiti sakamakon raunukan da suka samu.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta tiso keyar mayan kwamandojin mayakan 'yan a ware zuwa Kamaru bayan da suka shiga tarayya ta Najeriya.
Wasu alkaluma da kamfanin dilancin labaren AFP ya fitar ta hanyar sanarwowin da mahukuntan Kamaru ke fitarwa sun nuna cewa tun farkon rikicin, jami'an tsaron kamaru 21 ne 'yan a ware suka kashe a yankuna biyu na masu amfani da harshen Ingilishi.