Jami'an Tsaron Kenya Sun Kame Daya Daga Cikin Manyan 'Yan Adawar Kasar
(last modified Fri, 02 Feb 2018 12:18:30 GMT )
Feb 02, 2018 12:18 UTC
  • Jami'an Tsaron Kenya Sun Kame Daya Daga Cikin Manyan 'Yan Adawar Kasar

Jami'an tsaron Kenya sun kai farmaki gidan daya daga cikin manyan 'yan adawar kasar da ke birnin Nairobi fadar mulkin kasar tare da kame shi a safiyar yau Juma'a.

Rundunar 'yan sandan Kenya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun kai farmaki gidan Miguna Miguna daya daga cikin manyan magoya bayan madugun 'yan adawar kasar Raila Odinga tare da kame shi a safiyar yau Juma'a kan zargin laifin halattar bikin rantsar da madugun 'yan adawar kasar a matsayin shugaban kasa lamarin da ya yi hannu riga da kudin tsarin mulkin kasar.

A bayan kame Miguna Miguna magoya bayansa sun fito kan manyan hanyoyi a birnin Nairobi fadar mulkin kasar suna kone-konen tayoyi domin nuna rashin amincewarsu da kame dan adawar kasar.