Ana Ci Gaba Da Kame 'Yan Adawa A Sudan
Jami'an Tsaron Sudan na ci gaba da kame da shugabanin kungiyoyin siyasa, masu rajin kare hakin bil-adama, 'yan jaridu, biyo bayan zanga-zangar adawa da hauhawar farshin kayan masrufi a kasar
Kamfanin dillancin Labaran Irna na kasar Iran ya habarta cewa jami'an 'yan sandar kasar Sudan na ci gaba da kame shugabanin jam'iyun siyasar na bangare adawa , biyo bayan zanga-zangar baya-bayan da 'yan kasar suka yi na nuna rashin amincewar su da karin farashin kayan masrufi a kasar.
A jiya Alhamis, jami'an 'yan sanda sun yi awan gaba da Saleh Mahmoud al-Mahami gungu a kwamitin jam'iyar 'yan ra'ayin gurguzu na kasar da Fadlullah Barmat Nasser mataimakin shugaban jam'iyar Al-Umma na kasar.
A watan janairun da ya gabata, gwamnatin ta sudan ta kame Mohamed Mukhtar al-Khatib babban saktaren jam'iyar masu ra'ayin gurguzu na kasar da Omar Al-Daghir shugaban jam'iyar Congress ta kasa, da Sara Afdallah saktariya ta jam'iyar Al-Umma, da Abraham Al-Amin,da Mohamed Abdullah al-Dawma dukkanin su shugabani ne na jam'iyar Al-umma ta kasar.
'Yan adawar gwamnatin ta sudan na ganin cewa wannan kame-kamen da gwamnatin ta Sudan ke yi ba zai hana su ci gaba da neman hakin su ba ta hanyar zanga-zangar lumana a kasar ba.
Tun a farkon watan janairun da ya gabata ne 'yan kasar ta Sudan suka fara gudanar da zanga-zangar adawa da sabon tsarin tattalin arzikin gwamnatin kasar bisa zartar da siyasar Asusun lamuni na Duniya.