An ceto ma'aikatan hako zinare 955 a Afrika ta kudu
Ma'aikatan ceto a Afirka ta Kudu sun sami nasarar ceto dukkan ma'aikatan hakar ma'adai su 955 wadanda suka makale a karkashin kasa sakamakon katsewar wutar lantarki a mahakar zinare ta Beatrix dake kasar.
A wannan juma'a ce ma'aikatan ceto suka samu nasarar ceto ma’aikatan hako zinare 955 da suka makale cikin karkashin kasa tun a jiya Alhamis.
Kamfanin da mai’akatan ke wa aiki, mai suna Sibanye-Stillwater, ya ce kakkarfar guguwa ce ta haddasa katsewar lantarki a filin hakar ma’adanan da ke kauyen Theunissen da ke gaf da birnin Welkom.
Mai Magana da yawun kamfanin hakar ma’adanan, James Wellsted ya tabbatar da cewa ma’aikatan su 955 da ke makale cikin karkashin kasar, sun samu kulawa da ta dace, .
Wellsted ya ce kwararru sun taimaka wajen gyara matsalar lantarkin tareda samar da hanyar ceto ma’aikatan, wadanda tun a jiya aka samu nasarar zakulo 272.
Zurfin ramin hako zinaren da ma’aikatan suke ciki mai dauke da matakai 23, ya kai mitoci dubu daya.