Shugaban Masar Yana Fuskantar Suka Sakamakon Bankado Alakar Gwamnatinsa Da H.K.Isra'ila
Shugaban kasar Masar ya fara fuskantar tofin Allah tsine sakamakon bankado alakar da gwamnatinsa take gudanarwa a boye da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila.
Shafin watsa labaran Arab 21 ya watsa rahoton cewa: Jam'iyyun siyasa da kungiyoyi masu zaman kansu musamman na fararen hula a Masar sun fara yin tofin Allah tsine kan matakin da shugaban kasar Abdul-Fatah Al-Sisi ya dauka na kulla alaka a boye da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila.
Rahoton ya bayyana cewa: Shugaba Al-Sisi ya bai wa jiragen saman yakin gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra'ila damar kaddamar da hare-haren soji kan yankunan lardin Sina ta Arewa da sunan fada da 'yan ta'adda, inda yau tsawon shekaru fiye da biyu jiragen saman yakin Haramtacciyar Kasar Isra'ila suna luguden wuta kan yankunan lardin na Sina.
Kungiyar ta'addanci ta Baitu- Maqdis da ta shelanta hadewarta da kungiyar ta'addanci ta Da'ish ita ce ta yi kaurin suna a fagen kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan yankin na Sina na kasar Masar.