Kenya : An Bude Gidajen Talabijin 2 A Aka Dakatar
A kasar Kenya, biyu daga cikin goddajen talabijin uku da gwamnatin kasar ta dakatar watsa shirye shiryensu a ranar 30 ga watan da ya gabata sun fara aiki a yau Litini.
Tashohin biyu da suka fara aiki a yau, sun hada da NTV da kuma KTN News, saidai har yanzu guda daga cikinsu wato Citizen TV na ci gaba da kasancewa a rufe.
An dai dakatar da watsa shirye shiryen gidajen talabijin din uku ne a karshen watan da ya gabata a lokacin da suke watsa bikin rantsar da jagoran 'yan adawa na kasar Raila Odinga a matsayin shugaban al'umma na kasar kai tsaye.
Ministan cikin gida ksar ya shaida a lokacin dakatar da gidajen talabijin din cewa an rufe su har sai an kammala wani bincike da ake gudanar wa akansu.
Shi ma dai Ministan tsaron kasar Fred Matiang’i, ya zargi wasu kafafen yada labarai wajen taimakawa da ingiza rikici a kasar.