Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnatin Afirka Ta Kudu
Wasu kungiyoyin fararen hula da 'yan siyasa sun gudanar da zanga-zangar neman shugaba Zuma ya yi murabus daga kan mukaminsa a daidai lokacin da jam'iyar ANC mai mulki ke gudanar da taro.
Kamfanin dillancin labaran Hukumar radio da talabijin na kasar kasar Iran ya habarta cewa a jiya Litinin daruruwan 'yan kasar Afirka ta kudu ne suka gudanar da zanga-zangar neman shugaba Jacob Zuma ya yi murabus daga kan mukaminsa a birnin Johannesburg.
Shugabannin jam'iyar ta ANC za su yi nazari kan shugabancin jam'iyar, tare da daukar matakai kan kudirin jam'iyun adawa da ke shirin kada kuri'ar yanke kauna kan shugaba Zuma a ranar 22 ga watan Fabrairu.
Akwai matsin lamba sosai akan Mista Zuma da ke neman ya sauka kafin ya gabatar da jawabinsa na shekara-shekara game da halin da kasar ke ciki.
A yanzu dai ANC na da burin shawo kan mastalar da ke addabar jam'iyar, domin kare martaba da tasirinta a babban zaben kasar da ke tafe.