Harin Ta'addancin Kungiyar Boko Haram A Arewa Maso Gabashin Najeriya
(last modified Tue, 06 Feb 2018 05:39:13 GMT )
Feb 06, 2018 05:39 UTC
  • Harin Ta'addancin Kungiyar Boko Haram A Arewa Maso Gabashin Najeriya

Majiyar tsaron Najeriya ta sanar da cewa kungiyar boko haram ta kai wani harin ta'addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto majiyar tsaron Najeriya a jiya Litinin na cewa mayakan boko haram sun kai wani hari a kauyen Alau-Kofa da ke kusa da garin Maiduguri babban birnin jahar Borno dake shiyar arewa maso gabashin kasar tare da kashe akala mutame biyu.

Duk da cewa jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da samun narasa a kan mayakan na boko haram, sai dai a 'yan kwanakin nan, mayakan na boko haram na ci gaba da kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan Najeriya, Nijer da kuma Kamaru.

Tun a shekarar 2009 ne kungiyar boko haram ta fara kai hare-haren ta'addanci a yankunan arewa maso gabashin Najeriya, sannan kuma daga baya ta fadada kai hare-harenta a kasashen Kamaru, Chadi da jamhuriyar Niger.

Bisa kididdigar MDD, daga shekarar 2009 zuwa yanzu, rikicin boko haram ya ci rayukan sama da mutane dubu 20 a kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi sannan ya raba sama da mutane miliyan biyu da mahalinsu.