Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu Ya Amince Da Yi Murabus
(last modified Wed, 07 Feb 2018 12:30:07 GMT )
Feb 07, 2018 12:30 UTC
  • Shugaban Kasar  Afirka Ta Kudu Ya Amince Da Yi Murabus

Kafafen watsa labarun kasar Afirka Ta Kudu ne suka ambaci cewa shugaban kasar Jacob Zuma ya aminta da yin murabus bisa sharadi

Jaridar Times ta Afirka Ta Kudun ta ce Zuma ya cimma matsaya da mataimakinsa -Cyril Ramaphosa cewa zai yi murabus idan aka samar da yanayin da ya dace.

Ana sa ran cewa a yau laraba ne Zuma zai gabatar da jawabi da a ciki zai yi magana akan yiyuwar saukarsa daga kan mukaminsa na shugabancin kasar ta Afirka Ta Kudu.

A zaben da aka yi na mukaman jam'iyya a watan Disamba na 2017, an zabe -Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban Jam'iyyar ANC mai mulki.

Wasu daga cikin 'yan jam'iyyar ta ANC da suka halarci tattaunawa a tsakanin Zuma da mataimakinsa, sun ce abin da yake so, shi ne samar da yanayin da zai sauka daga kan mukaminsa cikin mutunci.

Shugaban na Afirka Ta Kudu yana fuskantar tuhume-tuhume akan cin hanci da rashawa da kuma bannata dukiyar al'umma.