Hare-Haren Ta'addanci Sun Lashe Rayukan Mutane 3 A Kasar Somaliya
(last modified Wed, 07 Feb 2018 18:54:27 GMT )
Feb 07, 2018 18:54 UTC
  • Hare-Haren Ta'addanci Sun Lashe Rayukan Mutane 3 A Kasar Somaliya

Rundunar 'yan sandan Somaliya ta sanar da cewa: Wasu 'yan bindiga sun kashe mutane uku a hare-haren kisan gilla da suka aiwatar a sassa daban daban na birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.

Majiyar rundunar 'yan sandan Somaliya ta bayyana cewa: Wasu gungun 'yan bindiga sun aiwatar da hare-haren kisan gilla ta hanyar harbi da kananan bindigogi a sassa daban daban na birnin Mogadishu fadar mulkin kasar a cikin daren jiya wayewar garin yau Laraba, inda suka kashe mutane uku ciki har da jami'in tsaron kasar guda.

Majiyar tsaron kasar ta Somaliya ta daura alhakin kashe-kashen gillar kan 'yan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab ta kasar.

A gefe guda kuma rundunar sojin Somaliya ta yi nasarar kame wasu gungun 'yan ta'adda ta mutane hudu da ake zargi da hannu a kashe kwamishinan 'yan sandan yankin Bulo-burte da ke yankin Hiran a tsakiyar kasar ta Somaliya. Kamar yadda rundunar sojin ta yi nasarar rusa wani makarkashiyar aiwatar da kisan gilla kan wasu jami'an gwamnatin kasar a yankin na Hiran.