MDD: Fiye Da Mutanen Libya Miliyan Daya Ne Suke Bukatar Agaji
Feb 08, 2018 12:18 UTC
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa tana da bukatuwa da dalar Amurka miliyan 313 domin taimakawa mutanen Libya miliyan guda a cikin 2018
Tashar talabijin din Majalisar Dinkin Duniya ta ambato mai kula da ayyukan agaji ta Majalisar, Maria Do Valle Ribeiro ta ce; Za kuma a mai da hankali wajen bada kariya da lalata nakiyoyin da aka dasa,da suke daukar rayukan mutane.
Yankin gabacin kasar ta Libya wanda ya kasance a cikin yaki na tsawon shekaru uku, yana fama da matsalar nakiyoyin da aka dasa, wadanda suke daukar rayuka.
Maria do Valle Ribeiro ta kara da cewa; Yakin da ake ci gaba da yi a kasar ya sa mutane da dama na da bukatar agaji
Tags