Gwamnatin Chadi Ta Dakatar Da Wasu Jam'iyun Adawa A Kasar
(last modified Thu, 08 Feb 2018 17:55:55 GMT )
Feb 08, 2018 17:55 UTC
  • Gwamnatin Chadi Ta Dakatar Da Wasu Jam'iyun Adawa A Kasar

Gwamnati kasar Chadi ta dakatar da wasu jam'iyyun adawa guda 10 bisa zarginsu da tayar da tarzoma a tsakanin al'ummar kasar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin kasar Chadi ta ce ta dauki matakin dakatar da wasu jam'iyun bangaren adawa kimanin 10,sanadiyar ingiza al'umma na tayar da tarzoma a kasar.

Matakin gwamnati ya biyo bayan zanga zangar kungiyoyin kwadago da jami'yyun suka jagoranta dangane da matakin tsuke bakin aljihu na gwamnatin.

Acewar ministan tsaron Chadin Ahmat Mahamat Bachir, an dakatar da ayyukan jam'iyyun na tsawon watanni biyu, saboda abun da ya kira dalilai na tsaron kasa.

Ko baya ga hakan, hukumomin kasar ta Chadi sun sanar da haramta jerin gwano da ake shirin yi akan tituna a wannan Alhamis a karkashin jagorancin kungiyoyi masu zaman kasansu da na kwadago da jam'iyyun adawa.