Kasashen Afrika 8 Ke Halartar Gasar Olympics Ta Hunturu
An bude gasar wasanin Olympics na hunturu 2018 a birnin Pyeongchang na Koriya ta Kudu, inda a wannan karo aka samu karin kasashen Afrika dake halartar gasar.
'Yan wasa 12 ne daga kasashe takwas na nahiyar Afrika, da suka da Afrika ta Kudu, Eritrea, Ghana, kenya da Madagaska, da Marocco da Najeriya da kuma Togo ke halartar wasannin karo na 23 da aka fara yau 9 ga watan Fabariru zuwa 25.
'Wannan dai shi ne karon farko da aka samu yawan kasashen Afrika kamar haka da suka shiga wasannin gasar ta Olympics na Hunturu, indan aka kwatantan da shekaru biyar da suka gabata, duk da cewa mafi yawan 'yan wasan ba wai sun fito daga kasashen ne ba suna zaune a kasashen yamma da Amurka ne.
A shekara 2014 kasashen Afrika biyar ne suka halarci gasar a birnin Sotchi na kasar Rasha.
Kasashen Najeriya da Eritrea wannan karon farko ne suke halartar wasannin, Najeriya na da 'yan wasa uku a yayinda Eritrea ke da guda da ya halarci wasan daga Canada.