Tanzaniya Ta Janye Daga Shirin Taimakawa 'Yan Gudun Hijira
Kasar Tanzaniya ta sanar da janyewa daga wani shirin Majalisar Dinkin Duniya na taimakawa 'yan gudun hijira.
Tanzaniya dai ta jima tana karbar 'yan gudun hijira a kasarta inda yanzu haka take karbar 'yan gudun hijira Burundi da Jamhuriya Demukuradiyyar Congo su 350,000 da suka tsarewa rikici a kasashensu.
Shugaban kasar Tanzaniya, John Magufuli, ya bayyana cewa matakin da kasar ta dauka na janyewa daga shirin na taimakawa 'yan gudun hijira na MDD na da nasaba ne da tsaro da kuma matsalar kudi.
A bara dai kasar Tanzaniya ta tsaida shirin yin rajistar bakin hauren, tare da umurtar 'yan Burundi dasu fice daga kasar, matakin da ya janyo mata suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama.
A halin da ake ciki dai MDD, ta sanar da aikewa da wata babbar tawaga domin tattaunawa kan batun da gwamnatin Tanzaniyar.