Kamaru : An Ayyana Dokar Ta Baci A Yankunan 'Yan A Ware
(last modified Sun, 11 Feb 2018 05:17:33 GMT )
Feb 11, 2018 05:17 UTC
  • Kamaru : An Ayyana Dokar Ta Baci A Yankunan 'Yan A Ware

Gwamnatin Kamaru, ta ayyana dokar ta baki a yankunan masu magana da harshen turancin Ingila, bisa fargabar hare hare na 'yan a ware.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce, an ayyana dokar ta bacin ne saboda babbar barazar kai hare hare a yankin daga masu fafatukar a ware.

Dokar dai ta tsawan mako guda, ta tanadi hana fitar dare daga karfe takwas na dare zuwa shida na safe a yankunan biyu na masu magana da harshen Ingilishi dake iyaka da Najeriya, inda hukumomin kasar ke zargin 'yan a ware da kafa sansani.

Al'amuran tsaro dai a yankunan sun tabarbare tun bayan da aka tiso keyar wasu 'yan a ware 47 da ake cafke a Najeriya ciki har da jagoransu Sisiku Ayuk Tabe.

Wannan dai na zuwa ne a daidia lokacin da kasar ta kamaru ke bikin ranar 11 ga watan fabarairu, ranar da zaben raba gardama da yi nasara hada yankunan masu magana da harshen Faransaci da kuma Ingilishi a rana irin ta yau a 1961, wacce akewa taken ''bikin matasa'' a kasar, bikin da 'yan a ware suka sha alwashin kawo masa cikas.