Mutane 4 Sun Hallaka Sanadiyar Tashin Nakiya A Kasar Mali
Tashin nakiya ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu 18 na daban a wasu garuruwa na yankin Mopti dake kasar Mali.
Kafafen yada labaran kasar Mali sun sanar da cewa wasu fararen hula hudu sun rasa rayukansu yayin da wasu 18 na daban suka samu munanan rauni yayin da motar da suke ciki ta bi ta kan wata nakiya, a yankin Mopti, wannan lamari na zuwa bayan makwanni biyu da rasuwar wasu matafiya 26 sakamakon tashin nakiya a kasar ta Mali.
Tashin nakiyar ya faru ne a ranar Juma'a a kan hanyar dake tsakanin garuruwan Dera da Konna da ke yankin Mopti in da 'yan ta'adda suka tsananta kai hare-hare a cikin kwanakin nan.
A shekara ta 2013 rundunar sojojin kasar Faransa suka kai dauki kasar ta Mali inda kuma suka yi nasarar korar gungun 'yan ta'adda masu nasaba da kungiyar Al-Qaeda daga 'yankin arewacin kasar ta Mali.