Jami'an Tsaro Sun Cafke Wasu Manyan 'Yan Ta'adda A Kasar Tunisia
Ma’aikatar harkokin cikin gida a Tunisia ta sanar da kame wasu ‘yan ta’adda masu maukar hadari su 5 a garin Dar Dima da ke cikin gundumar Jandawiyyah.
Kamfanin dillancin labaran INA ya habarta cewa, a jiya ma’aikatar harkokin cikin gida a Tunisia ta sanar da cewa jami’an tsaron kasar sun kame wasu ‘yan ta’adda masu maukar hatsari a garin Dar Dima da ke cikin gundumar Jandawiyyah a yammacin kasar.
Bayanin ya ce an kame mutanen ne bayan samun wasu bayanan sirri dangane da wani shiri da suke da shi na kaddamar da wasu hare-haren ta’addanci a wasu yankunan kasar, kamar yadda kuma aka same su da hannu a wasu hare-haren da aka kai a lokutan baya.
Kasar Tunisia dai ita ce kasa ta biyu bayan saudiyya, wajen yawan 'yan ta'addan takfiriyya masu dauke da akidar wahabiyanci da suke yaki a kasashen Syria da Iraki da sunan jihadi.