Feb 14, 2018 12:04 UTC
  • Sama Da Bakin Hure Dubu 8 Ne Suka Shiga Turai

Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta kasa da kasa ta sanar da cewa daga farkon wannan shekara ta 2018 zuwa yanzu, bakin haure dubu takwas da 154 ne suka shiga cikin kasashen Turai

A cikin wani rahoto da ta fitar a jiya talata, hukumar ta kara da cewa akwai kimanin mutane 401 da suka rasa rayukansu a tekun Bahrum yayin da suke kokarin isa zuwa kasashen na Turai.

Rahoton ya ce daga cikin mutanan da suka shiga Turai, dubu 4 da 731 ta hanyar kasar Italiya ne , sannan dubu daya da 729 ta hanyar kasar Girka ne, wasu dubu daya da 683 sun shiga turan ne ta hanyar kasar Sapaniya.

Hukamar ta ce idan aka kwatamta da wadanda suka shiga kasashen turan a shekarar 2017 din da ta gabata, adadin ya ragu sosai.

Rikicin gabas ta tsakiya da kuma matsalar tallauci a wasu kasashen Afirka da Asiya shi ne dalilin dake sanya wasu mutanan na barin kasashen su domin samun rayuwa mai kyau a kasashen Turai.

Tags