Jagoran 'Yan Adawa Na Zimbabwe Ya Rasu
Feb 15, 2018 05:51 UTC
Babbar Jam'iyyar adawa ta (MDC), A Zimbabwe, ta sanar da rasuwar jagoran ta, Morgan Tsvangirai, da yammacin ranar Laraba.
Marigayin, ya rasu ne bayan ya yi fama da ciwon kansar babban hanji, kamar yadda mataimakin shugaban jam'iyyar MDC Elias Mudzuri ya sanar.
Tsvangirai ya rasu ne a wani asibitin birnin Johannesburg, na Afrika ta Kudu, inda yake karbar jinya.
Jagoran 'yan hamayyan na Zimbabwe ya rasu yana da shekaru 65 a duniya, bayan ya shafe shekaru masu yawa yana adawa da tsohon Shugaban Kasar Robert Mugabe.
A lokacin yana raye, Mista Tsvangirai, ya taba taba zama firaministan kasar, har ila yau, ya sha dauri a lokuta daban-daban a karkashin mulkin Shugaba Mugabe.
Tags