Murabus Din Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu.
(last modified Fri, 16 Feb 2018 06:54:30 GMT )
Feb 16, 2018 06:54 UTC
  • Murabus Din Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu.

Murabus Din Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu.

 

Shugaban kasar Afirka ta kudu ya sannar da yin murabus ta wani bayani da ya yi wa al'ummar kasar ta kafafen watsa labaru. Bugu da kari Zuma ya ce; Jam'iyyarsa ta ANC ta yi masa matsin lamba da ya sauka daga kan mukamin nashi a cikin sa'aoi 48, don haka ya zartar da cewa ba zai bari a zubar da jini ko kuma kan jam'iyyar ya rabu gida biyu ba saboda shi. A dalilin haka ya yanke yin murabus.

Watanni da dama da suka gabata ne aka fara yi wa shugaban kasar Afirka ta kudun matsin lamba akan ya sauka daga kan mukaminsa saboda tuhumar da ake yi masa ta cin hanci da rashawa. Sai dai a cikin makwannin bayan nan ne matsin lambar ya yi Kamari, musamman bayan zaben Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban jam'iyyar ANC.

Bugu da kari kasar ta fuskanci koma bayan tattalin arziki da tsanantar rayuwa ga 'yan kasa.

Mataimakin shugaban Bankin Raya Afirka, Charles Boma ya bayyana kasar Afirka Ta Kudu a matsayin wacce mummunar siyasarta ta tattalin arziki ba ta da kyawu don haka aka sami koma bayan ci gabansa.

 

Wannan yanayin ya sa masu sukar gwamnatin Zuma suna zarginsa da cin amanar kasa da kuma ayyukan Nelson Mandela wanda ya yanto da kasar daga mulkin wariya.

Jam'iyyarsa ta ANC ta fusata akan yanayin da Zuma ya jefa kasar wanda hakan ya sa ta daukar mataki akansa, domin kaucewa abin da zai iya biyo baya a yayin zabe.

Tare da farin jini da karbuwar da Jam'iyyar ANC take da shi, saboda rawar da ta taka wajen 'yanto da al'ummar kasar,amma a shekarun bayan nan ta sami koma baya. Zaben da aka yi na magattan gari a 2016 ya nuna yadda jami'yyar ta sami koma baya sosai. Sakamakon ya kasance wata manuniya ce akan yadda al'ummar kasar suka dawo rakiyar jam'iyyar.

Tare da cewa a baya Zuma ya yi alkawalin yin murabus amma duk da haka ya rika daga kafa. Watakila yanayin siyasa da aka shiga ne acikin wasu kasashen nahiyar kamar murabus din ROberet Mugabee da tsoron kada a kifar da shi, sun tilasrta masa yin murabus.