Masar : An Hallaka Masu Da'awar Jihadi 7 A Yankin Sina
Rundinar sojin kasar Masar ta sanar da kashe 'yan tada kayar baya bakwai a ci gaba da farmakin data kaddamar a yankin Sina, da nufin tsarkake shi daga duk wata barazanar ta'addanci.
Bayanan sun ce hudu daga cikin mayakan an hallaka su ne a yayin samamen da jami'an tsaro suka kai a mabuyarsu.
Haka zalika rundinar sojin kasar ta Masar, ta ce an kuma cafke mutane kimanin dari, an kuma gano rumbun makaman yaki da dama, wadanda sojojin suka lalata.
Saidai a ecwar labarin babu tabas akan yadda shirin ke gudana, kasancewar 'yan jarida basu samu damar shiga yankin ba, don ganewa idannunsu hakikannin abunda ke faruwa.
Yau sama da mako guda kenan da rundinar Sojin Masar ta kaddamar da wani katsaitacen samame mai manufar yaki da ta'addanci a duk fadin kasar, ciki har da yankin Sinai da ya jima yana fama da matsalar mayakan dake da'awar jihadi.