Nijar : An Rusa Kananan Hukumomi 3
Gwamnatin Nijar, ta rusa wasu majalisun zababun mashawartan kananan hukumomin guda uku da suka hada da Golle (Jihar Dosso), da Tesker (Jihar Zinder) da kuma na karamar hukumar Dakoro a Jihar Maradi.
Gwamnatin ta kuma tsige magajin garin Garagumsa dake Jihar Zinder daga mukaminsa saboda tafka babban laifi.
Ana dai zargin koraren magajin garin na Garagumsa, Maman Issaka da rubda ciki da dukiyar jama'a ko kaddarori, da cin bashi ba bisa ka'ida ba da kuma wasu batutuwa da suka shafi sayar da filaye.
Gwamnatin ta sanar da hakan ne a yayin taron majalisar ministocinta na jiya Juma'a, inda kuma ta dau matakin tsawaita wa da watannin, wa'adin zababun mashawarta da shuwagabannin kananan hukumominsu da kuma tawagar mashawarta ta musamman ta babban birnin Yamai.
A can baya dai akalla sau hudu ana tsawaita wa’adin shugabancin kananan hukumomi na tsawon watanni shida-shida.