Senegal : Kotu Ta Bukaci Daurin Shekaru 7 Ga Magajin Birnin Dakar
Wata kotu a birnin Dakar na kasar Senegal, ta bukaci daurin shekaru bakwai a gidan kaso ga magajin babban birnin Dakar, Khalifa Sall.
Mai shiga da kara na kotun, ya kuma nemi Mista Salla da ya biya diyya ta Bilyan biyar da 490 na kudin Sefa (CFA)
Magajin birnin Dakar, Khalifa Sall, wanda ake tsare da shi tun ranar bakwai ga watan Maris na shekara 2017 data gabata, ana masa shari'a ne kan zargin karkata akalar kudaden jama'a da yawansu ya kai Bilyan 1,8 na sefa.
Saidai lauyoyinsa zasu sake gabatar da wata bukata gaban babbar kotun Dakar a ranar Litini mai zuwa.
KO baya ga magajin birnin na Dakar, Khalifa Sall, da akwai wasu kansaloli bakwai na majalisar babban birnin kasar da suka gurfana gaban kotu su ma bisa harkar zubda ciki da kudaden jama'a.