Congo: 'Yan Bindiga Sun Kai Wa Yankin Kivo Ta Arewa Hari
Feb 18, 2018 08:35 UTC
Majiyar gwamnatin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta tabbatar da cewa masu dauke da makaman sun kai harin ne akan fararen hula a yankin Kivo ta arewa.
Kamfanin dillancin labarun Xinhua da ya nakalto labarin ya ci gaba da cewa mutane da dama ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 8 suka jikkata.
Yankunan gabaci da arewa maso gabacin kasar ta Demokradiyyar Congo suna a matsayin sansanonin kungiyoyi masu dauke da makamai na cikin gida da kuma kasashen makwabta.
A cikin shekaru 20 da suka gabata, yankin ya zama tushen rashin zaman lafiya a kasar ta jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
Da akwai dakarun Majalisar Dinkin Duniya wadanda suke taimakawa gwamnatin kasar domin ganin zaman lafiya ya dawo.
Tags