Mahukuntan Tunusiya Sun Samu Nasarar Kame Wasu Gungun 'Yan Ta'adda A Kasar
Jami'an tsaron Tunusiya sun samu nasarar kame wasu gungun 'yan ta'adda a sassa daban daban na kasar a cikin 'yan kwanakin nan tare da fara gudanar da bincike kansu.
Majiyar tsaron Tunusiya ta sanar da kame wasu gungun 'yan ta'adda na mutane hudu da suke da alaka da kungiyar ta'addanci ta Da'ish a garin Mahdiyyah, inda ake ci gaba da gudanar da bincike kansu domin tatsar bayanan sirri.
Har ila yau jami'an tsaron gwamnatin Tunusiya sun kai samame garin Sidi-Bozize da ke tsakiyar kasar Tunusiya, inda suka nasarar kame wasu gungun 'yan ta'adda da suke da alaka ta kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya kuma mafi yawansu daliban jami'a ne, don haka ana ci gaba da gudanar da bincike kansu.
Wannan samame ya zo ne a bayan wani mummunan dauki ba dadi da aka yi tsakanin jami'an tsaron Tunusiya da wasu gungun 'yan ta'adda a garin Bin Qardan da ke kusa da kan iyaka da kasar Libiya a kwanakin baya, inda aka samu hasarar rayukan mutane fiye da hamsin kuma mafi yawansu 'yan ta'adda.