Kwango:An Kai Hari Kan Ma'aikatan Kare Mahali.
Wasu 'yan bindiga sun yi konton bauta kan wasu ma'aikatan kare mahali tare da kashe wani adadi daga cikin su a jamhoriyar demokaradiyar kwango.
Gidan radio kasa da kasa na Faransa ya habarta cewa wasu 'yan bindiga sun buda wuta kan wata mota dake dauke da ma'aikatan kare mahali a arewa maso gabashin kasar jamhoriyar demokaradiyar kwango a jiya asabar.
An kai harin ne a yankin Beni, kuma a cewa hukumar kare mahalin kasar, mutane 6 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu shida na daban suka jikkata sanadiyar harin.
A cewar hukumomin kasar Kwango, dukkanin fasinjan dake cikin motar 17 ne kuma fararen hula, sannan bayan hakan an ji karar wani abu mai kara a wurin da aka kai harin.tuni dai gawamnati ta zargi gamayar 'yan tawaye na fafutukar kafa demokaradiya da ake kira da AFD.
Mista Paulin Tshikaya daraktar cibiyar kare mahali na kasar ya bayyana cewa kungiyar 'yan tawayen sun kai harin ne domin kwashe abinda wannan mota ke dauke da shi na ma'adinai da hakan zai ba su damar samun bukatunsu na kudi.