Takkadama Kan Sabuwar Dokar Haraji A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28341-takkadama_kan_sabuwar_dokar_haraji_a_nijar
A jamhuriya Nijar, sabuwar dokar haraji dake kunshe a sabon kasafin kudin kasar na bana, na ci gaba da tada jijiyoyin wuya tsakanin gwamnati da kungiyoyin fara hula.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Feb 19, 2018 05:13 UTC
  • Takkadama Kan Sabuwar Dokar Haraji A Nijar

A jamhuriya Nijar, sabuwar dokar haraji dake kunshe a sabon kasafin kudin kasar na bana, na ci gaba da tada jijiyoyin wuya tsakanin gwamnati da kungiyoyin fara hula.

A farkon wannan shekara ta 2018 ne dai sabuwar dokar harajin ta fara aiki, saidai tun kafin hakan wasu kungiyoyin fara hula a kasar suka yi ta kashedi akan 'yan majalisar dokokin da kada su amince da dokar dake kunshe a kasafin kudin kasar na bana.

A halin da ake ciki dai kungiyoyin fara hulu da wasu al'ummar kasar na ci gaba da nuna adawa da sabuwar dokar wadda a cewarsu tana yi wa halin da talakan kasar ke ciki tarnaki.

A cewarsu dokar ta fi shafan rayuwar talaka ne, maimakon manyan jami'ai dana gwamnatin kasar, a yayin da kuma a cewarsu dokar ta yi yafiya wa wasu manyan kamfanoni dake aiki a kasar kamar irinsu na hakar Urenium da na kamfanonin sadarwa na salula haraji.

An dai yi jerin zanga zangogi da gangami da dama na nuna adawa da sabuwar dokar a kusan duk illahirin manyan jihohin kasar.

An gudanar da irin wannan gangami a Yamai, da jihar Zinder da kuma Tawa, mahaifar shugaban kasar mai ci, lamarin dake nuna cewa kiran kungiyoyin fara hula ya samu karbuwa sosai.

A Yamai, babban birnin kasar hadin kan kungiyoyin fara hula na OSC, sun ce zasu ci gaba da jan daga har sai mahukuntan kasar sun janye wannan dokar ta haraji, inda yanzu haka suka kira wata gagarimar zanga-zanga a ranar 25 ga watan Fabrairun nan.

Hukumomin kasar ta Nijar dai basa kallon kungiyoyin dake shirya wadannan jerin zanga-zangogi da gangami a matsayin na farar hula, suna masu danganta su da 'yan koren jam'iyyun adawa dake neman tada zaune tsaye a kasar.

A wata sanarwa da suka fitar kwanan baya gungun jam'iyyu masu mulki, sun zargi 'yan adawa da kungiyoyin na fara hula da neman ruguza kasa.

A sanarwar da suka fitar ranar Laraba data gabata bangaren masu mulkin na MRN da jam' iyyun dake mara musu baya sun sha alwashin gudanar da tasu zanga zanga da gangami na nuna goyan bayan gwamnati a ranar 4 ga watan Maris mai zuwa.

Wannan dai shi ne ja-in-ja da aka shiga a kasar ta NIjar, tsakanin kungiyoyin fara hula da gwamnatin kan sabuwar dokar ta haraji.

A halin da ake ciki dai babbar kungiyar kwadago ta kasar CGT- Niger, ta yi kira ga magoya baya da mambobinta dasu marawa kungiyoyin fara hula baya akan gwagwarmayar da suke na ganin mahukuntan kasar sun janye wannan sabuwar doka da suka danganta da marar imani.

Yanzu dai ya rage a ga yawan fitowar jama'a a zanga-zangar da kungiyoyin fara hula suka kira a ranar 25 ga watan nan da kuma wacce gungun jam'iyyu masu mulki suka kira a ranar 4 ga watan Maris mai zuwa, ko da ya ke tuni aka fara zargin bangaren masu mulki da yunkurin yin amfani da kudi don samun halartar jama'a a zanga zangar da zasu gudanar nan gaba.