Gagarumar Matsalar Ruwan Sha A Kasar Afirka Ta Kudu
(last modified Mon, 19 Feb 2018 06:30:06 GMT )
Feb 19, 2018 06:30 UTC
  • Gagarumar Matsalar Ruwan Sha A Kasar Afirka Ta Kudu

Mahukuntan kasar Afirka ta kudu sun sanar da cewa, sakamakon karancin ruwan sama da ake fuskanta a mafi yawan yankunan kasar, hakan ya jefa kasar cikin mawuyacin hali na karancin ruwan da ake tarawa a manyan madatsun ruwa na kasar.

Jaridar Lomond ta kasar Faransa ta bayar da rahoton cewa, mahukuntan Afirka ta kudu sun danganta wannan matsala ne da farin da ake fama da shi shekaru uku a jere a kasar, wanda hakan yasa gwamnatin kasar ta sanar da cewa, za a yanke ruwan sha zuwa wasu yankunan kasar daga watan Yuni mai zuwa.

Rahoton ya ce ma'aikatar magajin gari a birnin Cape Town, daya daga cikin manyan biranan kasar Afirka ta kudu mai yawan jama'a da suka kai miliyan 4.5, ta sanar da cewa sakamakon wannan matsala ta karancin ruwa a manyan madatsan ruwa na yankin, daga nan zuwa watan Afirilu ne kawai za a iya samun wadataccen ruwan sha na fanfo.

Hukumomin Afirka ta kudu sun ce tun daga shekara ta 1921, kasar ba sheda mummunan fari irin wannan ba.