Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Ofishin Yansanda A Afrika Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28411-yan_bindiga_sun_kai_hari_kan_ofishin_yansanda_a_afrika_ta_kudu
Labaran da suke fitowa daga Afrika ta kudu sun bayyana cewa yan bindaga sun kai hari a kan ofishin yansanda a wani wuri a kudancin kasar a yau Laraba.
(last modified 2018-08-22T11:31:27+00:00 )
Feb 21, 2018 11:45 UTC
  • Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Ofishin Yansanda A Afrika Ta Kudu

Labaran da suke fitowa daga Afrika ta kudu sun bayyana cewa yan bindaga sun kai hari a kan ofishin yansanda a wani wuri a kudancin kasar a yau Laraba.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana cewa yan bindigan sun kai hari a kan wani ofishin yansanda a safiyar yau laraba sun kuma kashe jami'an yansanda 5 da soja guda. Banda haka yan bindigan sun kwace makamai masu yawa a ofishin yansandan suka yi gaba da su. 

Afrika da kudu dai tana daga cikin kasashen duniya wadanda yan bindiga suke yawan kashe jami'an tsaro . Labarin ya kara da cewa kididdigan baya-bayan nan ya nuna cewa daga wata Afrilun shekara ta 2016 zuwa maris na shekara 2017 an kashe jami'an tsaro kimani 57