G5 Sahel Ta Samu Cike Gibin Kudaden Da Take Bukata A Brussels
Kungiyar kasashen nan biyar na yankin Sahel, ta samu kudaden da take bukata a wani taro neman tallafi na kungiyar da ya gudana yau Juma'a a birnin Brussels na kasar Belgium.
Taron dai ya samu halartar shwuagabannin kasashen biyar na kungiyar da suka hada da (Mali, Nijar, Tchad, Mauritania da Burkina Faso) da kuwa wasu shuwagabannin kasashe da na gwamnatocin Turai kimanin talatin da suka isa Brussels don nuna goya bayansu ga kasashen na G5 akan anniyarsu ta yaki da ta'addanci a yankin na Sahel.
Bayanai sun nuna cewa tuni kungiyar ta cimma gurinta na kudaden da take bukata, Miliyan 414 na Wuro, don kuwa kungiyar tarayya turai da kasashen mambibinta sun alkawarta bada rabin kudaden, kan 250 da take da su.
Shugaban kungiyar ta G5 Sahel kana shugaban kasar Nijar, Isufu Mahamadu, ya ce wannan dama ce ta baiwa yaran yankin na Sahel da zabinsu biyu ne ko zuwa turai ko amsa kiran masu aikata muggan laifuka, makoma mai kyau.
Shugaba Isufu ya ce yaki da ta'addanci zai lashe kudade masu yawa don kuwa ko wacce shekara ana sa ran kashe Miliyan 115 na Wuro, kuma ba'a san tsawan lokacin da aikin zai dauka ba, don haka akwai aiki.