An Dage Dokar Hana Fitar Dare A Tunusiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i286-an_dage_dokar_hana_fitar_dare_a_tunusiya
A Watan janairu daya gabata ne aka ayyana dokar hana fita dare saboda zanga-zanga gama gari akan rashin aikin yi ga matasa
(last modified 2018-08-22T11:27:45+00:00 )
Feb 04, 2016 14:31 UTC
  • Shugaban kasar Tunusiya Beji Caid Essebsi
    Shugaban kasar Tunusiya Beji Caid Essebsi

A Watan janairu daya gabata ne aka ayyana dokar hana fita dare saboda zanga-zanga gama gari akan rashin aikin yi ga matasa

Hukumomi a Tunusiya sun sanar da dage dokar hana fita dare da aka ayyana a watan daya gabata sakamakon zanga-zanga da matasan kasar suke yi a lokacin saboda matsalar rashin aikin yi.

wata sanarwa daga ma'aikatar cikin gidan kasar ta bayanai cewa an dau wannan matakin ne, ganin kyautatuwar yanayin tsaro da aka samu a baya bayan.

Doka dai da aka dage an dai ayyana ta ne a ranar 29 ga watan January daya gabata, kuma ta shafi hana yawan dare daga karfe takwais na dare zuwa biyar na safe agogo wurin.

Zanga-zanga da aka fara a lokacin ta dai dauko asali ne a unguwar (Ettadhamen) bayan da wani matashi marar aikin yi mai suna Ridha Yahyaoui ya hau wani karfe wutar lantarki ya hallaka kan sa.